Japan

Prime Ministan Japan Naoto Kan ya yi Murabus

Prime ministan Japan Naoto Kan bayan kammala jawabin Murabus dinsa
Prime ministan Japan Naoto Kan bayan kammala jawabin Murabus dinsa © Reuters/Toru Hanai

Prime Ministan Japan Naoto Kan ya yi Murabus a wani mataki na bayar da damar gudanar da zaben sabon Primiya na shida a kasar.Kimanin ‘yan takara tara ne dai ke neman kujerar Kan, wadanda suka hada da tsohon Ministan harakokin wajen Japan Seiji Maehara, da Ministan Kudi Yoshihiko Noda wanda ya kaddamar day akin neman zabensa a ranar Assabar.Tun a watan Yuni ne dai Kan, ya bayyana cewa zai yi murabus amma da sharadin cim ma masu manufofinsa guda 3 da suka shafi kasafin kudi. Kuma a yau Juma’a ne aka gabatar da kudirin doka a gaban Majalisa wanda hakan ya tabbatar da yiyuwar yin Murabus din Noato Kan.Duk wanda dai aka zaba a matsayin sabon Prime Ministan Japan zai fuskanci kalubale da dama da suka hada da shawo kan matsalar cibiyar Nuclear tare da kokarin farfado da darajar tattalin arzikin kasar.