IMF

Dominique Strauss-Kahn ya ziyarci IMF

Dominique Strauss-Kahn tare da mai dakin shi, Anne Sinclair
Dominique Strauss-Kahn tare da mai dakin shi, Anne Sinclair REUTERS/Lucas Jackson

A wata ziyara da tsohon shugaban hukumar lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn, ya kai ziyara hedikwatar hukumar Lamunin ta duniya a karon farko tun bayan zarginsa da yiwa wata mata fyade, inda ma’aikatan hukumar suka karbe shi hannun biyu-byu, tare da jinjina masa,Strauss-Kahn, dai ya kai ziyarar ne tare da uwargidansa inda ya gana da wacce ta gaje shi Christine Lagarde, tare da zantawa da manemwa labarai a harabar hedikwatar.