Japan

An zabi sabon PM a kasar Japan

Sabon PM na Japan Yoshihiko Noda
Sabon PM na Japan Yoshihiko Noda Reuters/Toru Hanai

Majalisar kasar kasar Japan ta zabi tsohon Ministan kudin kosar Yoshi-hiko Noda a matsayin sabon Prime Minista. Tuni dai sabon Prime Ministan Yoshi-hiko Noda ya bayyana cewa zai farfado da darajar tattalin arzikin kasar, da ambaliyar ruwa da bala’in tsunami suka daidaita a watan Maris day a wuce, musamman kokarin yaki da darajar kudin Yen. Sabon Prime Ministan na da babban kalu bale a gaban shi, ganin yadda kasar ta yi Prime Ministoci shidda a cikin shekaru 5.