Thailand

Ambaliyar ruwa a Bangkok, Fira Minista ta yi kiran kwantar da hankali

Yankin  Ayutthaya a Thailand da annobar ambaliyar ruwa ta shafa
Yankin Ayutthaya a Thailand da annobar ambaliyar ruwa ta shafa REUTERS/Chaiwat Subprasom

Annobar ambaliyar ruwa ta shafi birnin Bangkok na Thailand inda daruruwan ‘yan kasar suka kauracewa gidajensu don kauracewa annobar, sai dai kuma Fira Ministar kasar ta yi kiran kwantar da hankali bayan ta jadadda katsewar sake aukuwar annobar.Wannan dai itace annoba mafi muni a Thailand da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 289 a yankin arewaci da tsakiyar kasar.Tuni mazauna arewacin Bangkok suka kauracewa gidajensu bayan wani gargadi da gwamnatin kasar ta yi na sake aukuwar annobar.Yanzu haka kuma Fira Ministar kasar Yingluck Shinawatra ta bayyana cewa gwamnati ta dauki matakan kare sake aukuwar ambaliyar.