Faransa-Afganistan

An fara janye dakarun Faransa daga kasar Afghanistan

AFP/Marai SHAH

Kusan sojojin kasar Faransa 200 ne yau Laraba suka bar Kabul babban birnin kasar Afghanistan zuwa gida, kuma sune na farko karkashin tsarin janye sojan Faransa daga kasar ta Afghanistan mai fama da tashe tashen hankula.A kan idanun ‘yan jaridu ne dai jirgin Sojan na Faransa ya cira daga birnin na Kabul.Nan zuwa karshe shekara mai kamawa ta 2012, ana saran sojan Faransa, kashi daya bisa hudu, ne za'a kwashe zuwa gida, sannan kuma a shekara ta 2014 ake saran za'a kammala kwashe dukkan sojan zuwa gida kasar Faransa.