Isra'ila-Hamas

Palesdinawa sun ce lokaci bai yi ba su fara tattaunawa da Isra’ila

Salam Fayyad, Fira Ministan Palesdinawa.
Salam Fayyad, Fira Ministan Palesdinawa. Reuters

Fira Ministan Palasdinu, Salam Fayyad, yace lokaci bai yi ba da zasu koma teburin sasantawa da Isra’ila, kamar yadda kungiyar kasashen da ke shiga tsakanin bangarorin biyu suka bukata.Kungiyoyin sun bukaci fara tattaunawar ranar 26 ga watan nan, a Birnin Kudus, amma Fayyad yace, duk wata tattaunawa da ba zata kai ga cim ma biyan bukata ba, to bata da amfani ga Palesdinawa.