Libya

Tarihin Hambararren Shugaban Libya Marigayi Gaddafi

Hambararren Shugaban kasar Libya Marigayi Muammar Gaddafi
Hambararren Shugaban kasar Libya Marigayi Muammar Gaddafi REUTERS/Huseyin Dogan/Files

An haifi Muammar Gaddafi da ake kira Kanal Gaddafi a ranar 19 ga watan Yuni na 1942 a kauyen Qasr Abu Hadi mai tazarar kilo mita 18 kudu maso gabashin birnin Sirte.Ya shiga aikin soja inda ya zama kusa a ciki kafin ya jagoranci kasar sakamakon juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin sarautar zura’ar al Sanussi a kasar Libiya a shekarar 1969.Ya share tsawon shekaru 42 kan madafan iko, inda ya assasa mulkin mai wuka da nama da ya sa ya zama shugaban kasar mafi dadewa kan karagar mulki tun bayan yakin duniya na biyu.A shekarar 1977 ya haifar da wani juyin juya hali wajen sake fasalta tsarin mulkin kasar wacce ta zama Jamhuriyar Larabawan Libiya mai bin tafarkin demokradiya irin wace ya assasa ta kai tsaye, a 1979 ya soke mukaminsa na zama shugaban kasa inda ya aiyana kansa na babban kwamandan Libiya shugaban juyin juya halin kasar.A bangaren siyasar kasashen duniya Gaddafi ya rike matsayin dan kishin Larabawa ko Nahiyar Afrika, kasashen duniya irinsu Faransa Amurka da Birtaniya sun zarge shi da zama mai shuka kungiyoyin yan ta’adda, da kuma tallafawa 'yan tawaye a duniya, wanda kuma aka dora wa nauyin harin jirgin Lokarbi 1988 da na UTA 1989. A farkon watan Febrairun wannan shekara ta 2011, mulkinsa ya hadu da barazana sakamakon zanga zangar da ta barke a wasu kasashen Larabawa wacce nan take ta juye zuwa yakin basasa a kasar ta Libiya, bayan da y'an tawaye CNT suka karbe garin Tripoli cikin watan Agustan na 2011, Gaddafi ya koma Sirte kafin su cimmashi su kashe a yau 20 ga wata Octoba na shekara ta 2011.