Saudiya
An yi jana'izar Yarima Sultan a Suadiyya
Wallafawa ranar:
Dubban jamaa daga sassan duniya yau suka hallara birnin Riyaldh na kasar Saudiyya inda akayi janaizar Yarima Sultan Bin Abdulaziz dan gidan Sarautar Saudiyya.Ranar Asabar ne Yarima Sultan ya rasu a wani asibitin birnin New York, na kasar Amirka, yana da shekaru 87.Cikin manyan bakin da akayi jana'izar a gaban su akwai Mataimakin Shugaban kasar Aurka Joe Bidan, Shugaban kasar Pakistan Asif Ali Zardari, Shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir, da PM Malaysia Najib Razak da wasu Shugabannin kasashen duniyan da dama.