Afghanistan

Mutane 10 sun mutu bayan Tankar Mai ta yi tuntube da Bom a Afganistan

Harin Bom a yankin Parwan
Harin Bom a yankin Parwan Reuters

Jami’an tsaro a kasar Afghanistan sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 10 bayan wata Tankar Man Fetir ta yi tuntube da kunshin Bom a arewacin kasar.Roshna Khalid mai Magana da yawun mahukuntan yankin Parwan tace wani bom ya sake fashewa bayan fitowar mutane wajen kwasar ganimar Man Fetir.Gwamnan Parwan yace mutane 10 sun mutu, wasu 25 kuma suka samu rauni.Har yanzu dai babu wadanda suka fito suka yi ikirarin daukar alhakin dasa bom din. Sai dai a arewacin Pakistan, kungiyar Taliban ta dala wani bom a wata tankar man Fetir ta dakarun Kungiyar NATO.