Yemen
Saleh a Yemen yace zai yi murabus
Wallafawa ranar:
Shugaban Kasar Yemen, Ali Abdallah Saleh, ya shaidawa Jakadan Amurka a Sanaa, cewa a shirye yake ya sauka daga karagar mulki, sakamakon ci gaba da tashin hankalin da ake samu a kasar.Bayan ganawar da suka yi da Jakadan, Gerald Feierstein, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Victoria Nuland, ta yaba da matakin, inda ta bukaci ya cika alkawari.