China-EU

Kasashen Turai suna neman taimakon China

Kawancen China da kasashen Turai
Kawancen China da kasashen Turai Getty Images/Cristian Baitg

Shugabannin kasashen Turai sun fara shawarwarin tunkarar kasar China domin neman tallafin kudaden da zasu ceto matsalar tattalin arzikin da ya shafi kasashensu.Ana tunanin China zata amince da bukatar Turai domin zuba hannun jarin kudi Dala Biliyan 100 a kasuwar kasashen. Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy yace shigar kasar girka cikin kasashen masu amfanin da kudin euro kuskure ne. A cewarsa kasar Girka tun da farko bata shirya ba a lokacin da kasar ta shiga kawance kasashen a shekarar 2001.Shugabannin sun kwashe sa’o’I a Brussels jiya Alhamis domin cim ma yarjejeniyar da zata kawo karshen matsalar tattalin arzikinsu.Yanzu haka kasar China tacet ana jiran matsayin kasashen Turai kafin ta zuba kudadenta da zai ceto darajar kasuwar kasashen.