Syria

Kasashen Larabawa sun bukaci kawo karshen zubar da jini a Syria

Shugaban kasar Syria Bashar Al Assad tare da Jassim Bin Jabr Al Sani
Shugaban kasar Syria Bashar Al Assad tare da Jassim Bin Jabr Al Sani Reuters

Kungiyar kasashen Larabawa sun gabatar wa gwamnatin Syria wani tsarin da zai kawo karshen zubar da jini a cikin kasar tsakanin gwamnatin kasar da masu zanga-zangar adawa da shugaba Bashar Al Assad.A yau litinin ake sa ran za’a ji tabakin shugaba Assad bayan ya amsa cewa zai amince da bukatar ‘yan adawa.Majalisar Dunkin Dunya tace mutane sama da 3,000 ne aka kashe bayan kwashe tsawon watanni bakwai ana zanga-zangar adawa da shugaba Bashar Al Assad.Shugaba Assad ya zargi kasashen Turai wajen assasa rikicin Syria kuma ya bayyana cewa daruruwan ‘yan sanda ne da sojoji suka mutu.A ganawar da kasashen larabawa suka yi a birnin Alkahira na Masar tare da wakilan bangaren gwamnati da ‘yan adawa, sun gabatar da wani tsari da suke tunanin zai kawo karshen rikici a kasar Syria.