Italiya

PM Kasar Italiya Berlusconi ya amince da ajiye aiki

PM Italiya Silvio Berlusconi
PM Italiya Silvio Berlusconi © Reuters

Sanarwar da Prime Ministan kasar Italiya Silvio Berlusconi, ya bayar na shirin yin murabus, ya jefa fagen siyasar kasar cikin halin rashin tabbas.Bayan ya yi ta musanata wannan matakin daga karshe Mr. Berlusconi ya mika wuya, inda ya bayyana cewa zai yadda kwallon mangwaro domin ya huta da kuda, da zaran an fara aiwatar da dokar da za ta taimaka wajen nemo mafita kan matsalar tattalin arzikin Nahiyar Turai.PM Berlusconi ya ce bayan ya yi murabus, yana fatar ganin shugaban kasar Giorgio Napolitano, ya rushe majalisar dokoki, tare da kiran sabon zabe. Amma dai shugaban kasar ne zai ci gaba da rike madafun iko, da zaran ya sauka inda za a kafa gwamnatin gamin gambiza.Tuni masu zuba hannun jari suka yi marhabun da wannan matakin, yayin da darajar kudin Euro ke ci gaba da farfadowa, amma jaridun kasar sun nemi yin taka tsantsan, domin halin rashin tabbas da siyasar kasar zai iya yin illa ga kasuwanni.A baya, an yi ta bayyana fargabar yuwuwar kasar ta Italiya, da ke ta uku a karfin tattalin arziki tsakanin kasashen Turai, za ta iya ta fadawa kangin bashi. A halin da ake ciki, wata tawaggar Tarayyar Turai ta isa kasar, domin sa ido kan yadda za a aiwatar da muhimman sauye sauyen tattalin arziki, bayan da hukumar Taryyar Turai, EU, da Asusun Lamani na Duniya, IMF, sun sa mata tsauraran matakai.