Italiya

PM Kasar Italiya Berlusconi ya amince da Murabus

PM Italiya Silvio Berlusconi
PM Italiya Silvio Berlusconi REUTERS/Tony Gentile

PM kasar Italiya Silvio Berlusconi ya amince ya yi murabus, da zaran majalisar kasar ta amince da fara aiwatar da sauye sayen da kungiyar Tarayyar Turai ta bukata kamar su matse bakin aljihu.Mr. Berlusconi da ya shafe kusan shekaru 20, ana damawa da shi fagen siyasar kasar, ya yi ta samun matsin lamban ajiye mukaminsa, sakamakon zargin lalata da cin hanci, sai a baya bayan nan matsalarlar tattalin arzikin kasar.Wannan sanarwar ta sa kasauwannin hannayen jarin Amurka da Asiya sun fara farfadowa a yau Laraba.Sanarwar da PM Italiya, Silvio Berlusconi ya bayar na shirin yi murabus ta sa farashin kudin Euro ya haura, in aka kwatanta shi da dalar Amurka.Wannan matakin da Mr. Berlusconi ya dauka, zai iya kawo karshen matsalolin siyasa da na tattalin arzikin kasar ta Italiya dake ta 3 a karfin arziki a Nahiyar Turai.