Iran

Iran tace zata yi amfani da karfinta ga duk wani matakin soji akanta

Ayatollah Ali Khamenei  na Iran tare da Shugaba Ahmadinajad
Ayatollah Ali Khamenei na Iran tare da Shugaba Ahmadinajad AFP PHOTO/HO

A Shafin Internet na shugaba Ayatollah Ali Khamenei, Iran tace zata mayar da martani da karfinta ga duk wani hari ko barazanar daukar matakin soja akanta bayan da Isra’ila ta yi kiran duniya wajen daukar mataki domin karya shirin makamashin Nukiliyar kasar.A cewar Shugaba Khamenei wannan sako ne zuwa ga makiyan Iran musamman Amurka da Isra’ila.Wannan kalaman na shugaban na zuwa ne bayan da gwamnatin Isra’ila tace zasu yi amfani da jiragen yaki domin tarwatsa gurin da Iran ke aiwatar da ayyukanta na Nukiliya.Kiyayya tsakanin Iran da Amurka da Isra’ila sai ci gaba da karuwa take tun bayan wani rehoto na Majalisar Dunkin Duniya dake gasgata shirin Nukiliyar Iran inda kuma da dadewa ne Iran ke musanta hakan.