Syria

Kasashen Larabawa zasu sake ganawa bayan dakatar da Syria

Taron kasashen Larabwa a birnin Al Kahira na Masar
Taron kasashen Larabwa a birnin Al Kahira na Masar REUTERS/Mohamed Abd El-Ghany

A ranar Laraba ne tarayyar kasashen Larabawa zasu sake ganawa domin sake tattaunawa kan rikicin kasar Syria bayan da kasashen kungiyar 22 suka yanke hukuncin dakatar da kasar daga cikin kungiyar.Kasashen larabwa sun samu yabo da jinjina daga kasashen yammaci dangane da matakin dakatar da kasar Syria, sai dai wannan ya yi sandiyar kai wasu sabbin hare hare a ofishin jekadancin kasashen waje a Damascus babban birnin kasar Syria.Bayan kammala taronsu a birnin Alkahira na kasar Masar kasashen sun ba kasar Syria wa’adin kwanaki 15 domin fito da wani tsarin sasanta zaman lafiya a cikin kasar.Ministan harakokin wajen kasar Algeriya Mourad Medelci yace sun dakatar da Syria ne na wuccin gadi amma idan kasar ta nemi shawo kan matsalolinta zasu janye wannan dakatarwar.Kasashe 18 ne cikin 22 suka kada kuri’ar amincewar dakatar da kasar Syria domin nuna gazawarta na kawo karshen zubar da jinin da ake yi a cikin kasar, sai dai kasashe uku ne da Syria da Yemen da Lebann suka kada kur’ar kin amincewa da matakin, kasar Iraqi kuma ta kauracewa zaman taron.