Kuwait

Masu zanga-zanga sun kutsa cikin majalisar Kuwait

Sheikh Nasser al-Mohammad al-Sabah Fira Ministan kasar Kuwait
Sheikh Nasser al-Mohammad al-Sabah Fira Ministan kasar Kuwait Reuters/Stephanie McGehee

Daruruwan ‘Yan kasar Kuwait ne suka mamaye majalisar kasar, inda ‘Yan Sanda suka yi arangama da masu zanga-zanga da ke neman ganin Fira Ministan kasar Sheikh Nasser al-Mohammad al-Sabah yin murabus daga mukaminsa.Jagoran masu zanga zangar, Mussallam al Barack, yace sun samu shiga Majalisar, kuma suna bukatar rusa majalisar baki daya.Dubban masu zanga-zanga ne ke gudanar da zanga-zanga a kowane karshen mako domin kalubalantar majalisar kasar da ‘yan kasar ke zarginta da cin hanci.Rehotanni na nuni da cewa ‘yan sanda a kasar sun tarwatsa masu zanga-zanga inda suka ba yawancinsu kashi.Masu zanga-zangar sun balle kofar shiga majalisar inda suka yi tururuwa cikin ginin majalisar tare da rera taken kasar.Masu zanga-zangar sun bukaci gwamnatin kasar aiwatar da sabbin sauye-sauye, inda suke kuken cewa gwamnatin tana kaucewa tsarin kundin mulkin kasar.