Turkiya

Gwamnatin kasar Turkiya ta Gargadi Mahukuntan kasar Siriya

PM Turkiya Tayyip Erdogan
PM Turkiya Tayyip Erdogan Reuters

PM kasar Turkiyya Recep Tayip Erdogan ya gargadi Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad da ya shiga taitayinsa domin kwanakin da suka rage masa a madafun ikon na gab da karewa.Sakamakon wasu bayanai dake nuna cewa ayarin wasu motocin alhazai biyu na Alhazan Turkiyya an tare su a Siriya, PM Tayip Erdogan, ya ce kememen da Shugaba Assad ya yi na kin hana kashe bayin Allah da Sojan kasar ke yi, na dama lisasafi.PM Tayip Erdogan ya ce duk wani shugaba ai karya ce ya ce da karfin tsiya ne zai mulki jama'a.