Jordan

Sarkin Jordan ya gana da Shugaban Palesdinawa

Sarki Abdallah na 2 na kasar Jordan yau Littini ya tattauna da Shugaban Palestinawa Mahmud Abbas a Ramallah, a wata ziyara ta farko yankin wannan yanki cikin shekaru masu yawa da Sarkin ya kai.Ziyarar na zuwa ne ana saura kwanaki kadan a gudanar da wani taro tsakanin kungiyar Fatah data Hamas dake Palestinu.Da suke magana da manema labarai, lokacin da Shugabannin biyu ke ganawa, Ministan waje na kasar Jordan Nasser Judeh, ya nuna goyon bayan kasar Jordan a kokarin ganin Paestinu ta zama wakiliya a Majalisar Dinkin Duniya.