Siriya

Hukumar Kare Hakkin Bil-Adam ta MDD ta nemi Mataki kan Siriya

Navi Pillay Shugabar Hukumar Kare Hakkin bil Adam ta MDD
Navi Pillay Shugabar Hukumar Kare Hakkin bil Adam ta MDD REUTERS/Denis Balibouse

Babbar jami’ar hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) Navi Pillay, a yau Jumma’a ta nace kan bukatar daukar matakan gaggawa a kan kasar Siriya, domin gurfanar da ita kan aikata laifukan cin zarafin bil Adama da take yi.

Talla

A yayin da MDD ta bayyana cewa, kawo yanzu mutane dubu hudu ne mahukuntan kasar ta Siriya ta kashe, tun bayan barkewar zanga zangar kin jinin gwamnatin Bashar Al-Assad a watan Maris din da ya gabata.

Depuis le mois de mars 2011, les Syriens exigent des réformes et manifestent dans tout le pays (photo prise le 18 novembre 2011).
Depuis le mois de mars 2011, les Syriens exigent des réformes et manifestent dans tout le pays (photo prise le 18 novembre 2011). Reuters /Handout

A daya bangaren kuma, mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden, dake ziyara a kasar Turkiya, ya nemi a cikin gaggawa Shugaba Bashar Al’Assad da ya sauka daga kan shugabancin kasar, tare da kafa gwamnatin rikon kwaryar da zata shirya wani sabon zabe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI