Iraqi

Iraqi ta bada sammacen cafke mataimakin shugaban kasa

Mataimakin shugaban kasar Iraq Tariq al-Hashemi wanda Gwamnatin kasar ta bada sammacin kamo shi
Mataimakin shugaban kasar Iraq Tariq al-Hashemi wanda Gwamnatin kasar ta bada sammacin kamo shi Reuters

Hukumomin Kasar Iraqi sun bada sammacin kama mataimakin shugaban kasar, Tariq al-Hashemi, a wani yanayi da ake ganin yana iya sanadiyar rushewar Gwamnatin hadin kan kasar.Sammacin ya biyo bayan zargin aikata ta’adanci da akewa mataimakin shugaban kasar, kuma tuni aka kama wasu jami’ansa.

Talla

Mabiya Sunni da ke Majalisar Ministoci sun ce, zasu kauracewa zaman Majalisar saboda sammacin.

Wannan matakin kuma na zuwa ne bayan da mabiya Iraqiya masu goyon bayan Hashemi da mataimakin Fira Minista Saleh Al Mutlak suka bayyana matakin kaurace zauren Majalisar kasar domin nuna adawa da Fira Ministan kasar Nuri al-Maliki da suke zargin yana kokarin mamaye gwamnatin kasar.

A ranar Lahadi ne Maliki ya bada umurnin tube Mutlak, kuma ana hasashen ‘yan Majalisu kasar zasu bi umurnin shi lokacin zaman Majalisar ranar uku ga watan Janairu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI