Malaysia

Kotun Malaysia ta wanke Anwar daga zargin luwadi

Madugun adawa a kasar Malaysia Anwar Ibrahim lokacin da yake gaisuwar girma ga magoya bayansa bayan kotu ta wanke daga zargin luwadi
Madugun adawa a kasar Malaysia Anwar Ibrahim lokacin da yake gaisuwar girma ga magoya bayansa bayan kotu ta wanke daga zargin luwadi . REUTERS/Bazuki Muhammad

Wata Kotu a kasar Malaysia ta wanke shugaban ‘Yan adawar kasar, Anwar Ibrahim, daga zargin luwadi da ake ma shi, shari’ar da ta kwashe shekaru biyu ana tafkawa. Mai shari’a Zabidin Mohammed Diah, yace babu gaskiya a shaidun kwayar hallitar da aka gabatar masa.

Talla

Hukuncin kotun a Kuala Lumpur ya zo ne bazata inda Anwar tsohon mataimakin Fira Minista ne da aka dakatar a shekarar 1998 tare da daure shi a gidan yari bayan zarginsa da aikata luwadi.

Daruruwan magoya bayansa ne suka yi dandazo a harabar kotun bayan da kotun ta wanke shi, domin taya shi murna kuma yawancinsu musulmai ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI