Iran

An kashe wani malamin kimiyar Nukiliyar Iran

Motar  Mostafa Ahmadi-Roshan malamin kimiyar Nukiliyar kasar Iran an daga ta sama kusa da inda Bom ya tashi
Motar Mostafa Ahmadi-Roshan malamin kimiyar Nukiliyar kasar Iran an daga ta sama kusa da inda Bom ya tashi REUTERS/IIPA/Sajad Safari

An kashe wani babban masanin kimiyar makamashin Nukiliyar kasar Iran, Mostafa Ahmadi-Roshan bayan dala masa bom a motarsa. Mahukuntar kasar Iran sun zargi kasar Isra’ila da kitsa harin inda suka danganta harin da wanda aka kai a bara.

Talla

Kamfnin dillacin labaran kasar ya tabbatar da mutuwar malamin mai suna Mostafa Ahmadi-Roshan, mai shekaru 32 na haihuwa kuma tsohon dalibi ne a Jami’ar binciken Mai wanda ya yi aikin kula da bangaren makamashin Nukiliyar kasar a Natanz.

Kamfanin dillacin labaran kasar ya ruwaito mataimakin gwamnan Tehran yana bayyana cewa wannan aikin Isra’ila ne.

Shedun gani da ido sun shaidawa kamfanin Dillacin labaran Reuters cewa sun ga lokacin da mutane biyu saman babur ke dasa bom a motarsa, kuma sun tabbatar da cewa har wani mutum kusa da motar ya mutu.

Yanzu haka kuma kasar Iran ta zargi Jami’an leken asirin kasar Birtanya da Amurka da Isra’ila da kulla harin wadanda suka sha alwashin kashe duk wasu masanan da ke kokarin inganta makamashin Nukiliyar kasar Iran.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI