Taiwan

Shugaban kasar Taiwan Ma ya sake lashe zaben shugabancin kasar

Shugaban Taiwan Ma Ying-jeou
Shugaban Taiwan Ma Ying-jeou REUTERS/Pichi Chuang

Shugaban kasar Taiwan Ma Ying-jeou ya sake lashe zaben shugabancin kasar na wa’adi na biyu na shekaru hudu, inda ‘yan adawa suka amince shan kayi.

Talla

Sakamakon ya nuna ci gaba da kusanci da kasar China, ‘yar takarar jam’iyyar adawa Tsai Ing-wen ta amince da sakamakon zaben na jiya Asabar. Shugaba Ma yana da fiye da kashi 51 cikin yayin da Uwargida Tsai ke da kashi 46 cikin 100.

Kasar China ta bayyana ci gaba da aiki tare da kasar Taiwan bayan nasarar da Shugaba Ma Ying-jeou mai goyon bayan mahgakuntan birnin Beijing ya samu a zaben jiya Asabar.

Ma wanda ya samu wa’adi na biyu na shekaru hudu, ya fadada dangangatar Taiwan da China yayin wa’adinsa na farko.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI