Iraqi

An Cafke masu tsaron Lafiyar Mataimakin Shugaban kasar Iraqi 16

REUTERS/Saad Shalash

Jami'an tsaron kasar Iraqi na tsare da wasu masu tsaron lafiyar mataimakin Shugaban kasar Tareq al-Hashemi dake gudun hijira, a wani al'amari da mataimakin Shugaban kasar ke cewa kitsa sharri kawai aka yi masa.

Talla

Shi dai mataimakin Shugaban kasar na boye ne a wani gari dake yankin Kurdistan bayan zargin da aka yi masa tsakiyar watan jiya na Disamba, da sojojin Amurka ke barin kasar, aka zarge shi da renon wasu gwanayen kisan mutane.

Bayanai daga Ma'aikatar Harkokin cikin gidan kasar na cewa bayan an kama wasu Dokarawan Mataimakin Shugaban kasar 16, sun gaskata zargin da ake yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI