Yemen

Fada tsakanin sojan Yemen da tsageru masu dauke da makamai ya hallaka mutane 78

Wani Jami’in sojin kasar Yemen, ya ce adadin sojojin kasar da aka kashe a harin da 'yan kungiyar Al Qaeda suka kai musu, ya kai sojoji 78, yayin da su kuma suka kashe 'yan bindigan 25.

Talla

Rahotanni sun ce 'yan bindigan sun kai harin ne a wajen garin Zinjibar, dake Yankin Abyan, kuma yanzu haka mutane da dama sun samu raunuka.

Wani jami’in sojin kasar, ya shaidawa kanfanin Dillancin labaran Faransa cewar, adadin wadanda aka kashe na iya fin haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.