Isa ga babban shafi
Sri Lanka

Dan Sri Lanka da ya binne kansa ya mutu

Reuters/Stringer
Zubin rubutu: Suleiman Babayo | Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Wani Dan kasar Sri Lanka ya rasa ransa, yayin da yake kokarin kafa tarihi kan mutumin da yafi dadewa birne a karkashin kasa.

Talla

Janaja Basnayake, mai shekaru 24, ya birne kansa ne da taimakon iyalansa da kuma abokanansa, inda aka rufe shi da itatuwa da kuma kasa, amma sai rai ya yi halin sa.

Iyalan sun ce, an taba birne shi na sa’oi biyu, da sa’oi shida yana fitowa ba tare da matsala ba, amma a wanna karon, sai ya ce ga garun ku nan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.