Afghanistan-Amurka-Nato

Kungiyar taliban a Afghanisran ta ce sai ta dau fansar kisan fararen hular kasar 16 da wani sojan Amruka ya yi,

Kungiyar Taliban a kasar Afghanistan ta yi rantsuwar daukar fansa kan kisan fararen hular kasar 16, da suka hada da mata da kananan yara  da wani sojan Amruka ya yi a jiya lahadi a yankin kudancin kasar.  Wannan alkaba’in dai ya sake kwabar da raunannar huldar dake tsakanin kasar Amruka da Afghanistan. Wasu majiyoyi a Afghanistan da na kasashen yammaci sun bayyana cewa, a tsakar daren jiya lahadi ne, wani sojan kasar Amruka a rundunar tsaro ta Nato a kasar Afghanistan (Isaf) ya zare jiki daga sansaninsu na Kandahar, yankin da ke da yan Taliban, dauke da makamai, inda ya karkashe wasu mazauna gidaje 3 dake kauyukan dake kewaye da sansanin na Nato, mutanen da suka hada da kananan yara 9 da kuma wasu mata 3 tare da kona gawawwakinsu.Wannan ta’asa dai ta zo ne, wasu yan makwanni da wani sojan Amrukan ya wulakanta Alkur’ani mai tsarki a garin Bagram dake arewacin kasar Afghanistan, al’amarin da ya haifar da tashin hankalin zanga zangar kin jinin Amerikawa, da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 40 a kasar.