MDD ta nuna damuwa halin da ake ciki a Syria
Wallafawa ranar:
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki Moon, ya bayyana halin da ake ciki a kasar Syria a matsayin abinda ba za’a amince da shi ba, inda ya bukaci wakilan kwamitun Sulhu su hada kansu akan matsalar.Kalaman Sakataren na zuwa ne a dai dai lokacin da kwamitin ke shirin gudanar da wani taro yau Talata, dan amincewa da wani sabon kudiri akan Syria, muddin taki aiwatar da shawarwarin Kofi Annan, wanda aka nada a matsayin manzon musamman na MDD da kungiyar kasashen Larabawa.
Kasar Rasha ta bukaci Syria ta zagaita wuta, dan baiwa jami’an agaji kai kaya ga mabukata a cikin kasar, yayin da ta musanta cewar, bata da jirgin yaki a gabar ruwan Syria.
Ma’aikatar harkokin wajen Rasha, ta ce jirgin dake gabar ruwan Syria tankin mai ne, amma ba jirgin yaki ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu