Annan zai sake kai ziyara Syria, inji Ban Ki-moon
Wallafawa ranar:
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon yace nan bada jimawa ba ne Jakadan Majalisar na musamman, Kofi Annan zai sake kai ziyara kasar Syria, bayan yunkurin amincewa da wani kudiri a kwamitin Sulhu, ya samu kin amincewar Rasha.
Sanarwar da Ban Ki Moon ya bayar, na zuwa ne kwana guda bayan yunkurin kasashen Yammacin duniya na amincewa da wani sabon daftari kan Syria ya ci tura, saboda bai wa shugaba Bashar al Assad wa’adi.
Mista Ban yace bukatar su ita ce, na farko a kawo karshen kashe kashen da ake yi a Syria, na biyu a samu fahimtar juna tsakanin bangarorin kasar, don shata sabuwar makoma, na uku kuma akai kayan agaji ga mabukata a cikin kasar.
Sakataren wanda ke jawabi ga dakarun samar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Indonesia, yace ba za’a ci gaba da amincewa da halin da ake ciki a kasar Syria ba.
Rahotanni sun ce, kasashen Yammacin duniya na gyara akan daftarin da Russia ta ki amincewa da shi, dan sake tattaunawa yau.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu