Syria

Manyan Kasashe zasu dauki mataki kan rikicin kasar Syria

Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama 路透社

Shugaban Kasar Amurka, Barack Obama, da takwaransa na Rasha, Dmitry Medveev, sun bayyana shirin su na goyan bayan matakin diplomasiya dan magance zub da jinnin da ake samu a Syria.Bayan ganawar da shugabanin suka yi yau, shugaba Obama ya ce daya daga cikin manyan batutuwan da suka tattauna shine yadda za’a magance rashin fahimtar junan dake tsakaninsu kan tashin hankalin kasar Syria, inda suka cimma matsaya.

Talla

Obama ya ce, sun amince su goyi bayan Kofi Annan, na ganin ya samu nasarar shiga tsakanin da aka sa shi, dan samun halartaciyar Gwamnati, a ganawar da ita ce ta karshe tsakanin Medvedev da Obama, wanda zai kawo karshen mulkin sa a watan Mayu.

Kwamitin Annan ya bukaci tsagaita wuta, da kuma janyewar manyan makaman gwamnati daga Yankunan 'yan Tawaye, da kuma barin kai kayan agaji sa’a biyu kowacce rana.

Har ila yau ya bukaci sakin daukacin wadanda aka kama a rikicin na shekara guda.

Obama ya kuma ce, sun tattauna kan Iran, inda suka cimma matsayin sake komawa teburin shawara da kasar Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI