Syria-MDD

kasar Syriya zata ci gaba da mutunta yarjejeniyar tsagaita buda wuta

Centro histórico da cidade de Homs, foco da contestação do regime de al-Assad, está destruído pelos bombardeios do Exército.
Centro histórico da cidade de Homs, foco da contestação do regime de al-Assad, está destruído pelos bombardeios do Exército. REUTERS/Karam Abu Rabeh/Shaam News Network/Handout

Ministan Waje na kasar Syria Walid Muallem yace ko shakka babu kasar Syria zata mutunta yarjejeniyar zaman lafiya da komitin Kofi Annan ya gabatar.Ministan ya fadawa wani taron manema labarai a Damascus cewa, suna da ra’ayin tsagaita buda wuta, da janye Dakaru da kayan fada da aka girke a wurare, sannan kuma a baiwa ayarin masu sa idanu na MDD dukkan hadin kai da suke bukata. Ya zuwa yanzu dai ‘yan kalilan ne daga cikin masu sa idanun suka riga suka isa a kasar ta Syria.