Pakistan

Likitocin Pakistan sun yi nasarar ceto rayuwar wani jariri da aka Haifa da kafa Shida

Hoton Jaririn da aka haifa da kafa Shida a Pakistan
Hoton Jaririn da aka haifa da kafa Shida a Pakistan AFP

Likitoci a kasar Pakistan sun ce sun samu nasarar ceto rayuwar wani jariri da aka Haifa da kafa Shida a kasar bayan an yi masa aikin tiyata inda aka cire kafa hudu daga Shida.

Talla

Tawagar Likitoci Biyar ne suka aiwatar da aikin Tiyatar a Wata Asibiti a birnin Karachi, kuma Jamal Raza yace jaririn yana cikin koshin Lafiya bayan kammala aikin Tiyatar.
An haifi Jaririn ne a birnin Sukkur, mai nisan Kilomita 450 da Arewacin Karachi.

Likitoci sun ce wannan al’amari ana gadonsa ne amma yakan shafi jariri daya cikin Miliyan da za’a Haifa.

Mahafin Jaririn Imran Shaikh dai yana cikin farin ciki da Murna bayan ceto rayuwar dansa. Kuma ya shaidawa manema labarai fatar ganin jaririn ya rayu tare da kasancewa cikin koshin Lafiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.