Syria-Tashin Hankali
An wayi gari cikin wani sabon tashin hankali a kasar Syriya, duk da kasancewar tawagar masu zura ido a kasar.
Wallafawa ranar:
Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasar Syriya ta bayyana cewa, a tashin hankalin na yau an kashe dakarun gwamnatin kasar Syriya 12, fadan an gwabza shi ne a yau talata tsakanin dakarun gwamnatin kasar da yan tsageran dake adawa da gwamnatin shugaban kasar Bashar al-Assad, a garin Deir Ezzor.A cikin fadan da aka ce dakarun gwamnati sun yi amfani da tankokin yaki, Rokoki da kuma bindigogi masu sarrafa kansu amma duk da haka sun dandani hasarar rayukan dakaru sama da 10.