Bama

Suu Kyi ta karbi rantsuwar kama aiki a Majalisar dokokin kasar

San Suu  na rantsuwar kama aiki a majalisar dokoki
San Suu na rantsuwar kama aiki a majalisar dokoki REUTERS/Soe Zeya Tun

Jagorar yan adawar kasar Myanmar Uwargida Aung San Suu Kyi a yau ta yi rantsuwar kama aiki a matsayin wakiliyar Majalisar kasar, alamarin daya bude sabon babi a siyasar kasar.‘Yar shekaru 66 Aund San Suu Kyi tana cikin wakilai 33 na jamiyyarta ta National League For Democracy da aka zaba a watan jiya.Da take zantawa da manema labarai bayan ta yi rantsuwar, Suu Kyi ta ce, shakka babu zata sami bautawa jamarta.