Masar
Wata taho mu gama ta yi sanadiyar mutuwar mutane a kasar Masar
Wallafawa ranar:
Akalla sama da mutane 10 ne aka kashe a yayinda wasu da dama suka jikkata a cikin wata taho mugamar da ta hada yan adawa da magoya bayan sozojin dake mulki, a kusa da ofishin ma’aikatar ministan tsaron kasar Masarfadan da ake bukatar Sozojin kasar sun shiga tsakani wajen magance shi don gudun kar ya yadu a sauran sassan kasar ta Masar.Wakilin RFI a Alkahira Alexende Buccianti, ya ce, yau da kwanaki hudu ke nan ake yin wanan dauki ba dadi, a dandalin Abbasiya tsakanin mazauna unguwar da aka saba gudanar da zanga zangogin nuna goyan baya ga majalisar mulkin sojan kasar.