Syria

Akalla mutane 55 sun mutu, wasu 372 sun jikkata a wani harin kunar bakin wake a kasar Syriya

A Syriya wasu na dauke da gawar daya daga cikin mutanen da suka kone a wurin da aka kai harin a birnin Dams.10 mai 2012.
A Syriya wasu na dauke da gawar daya daga cikin mutanen da suka kone a wurin da aka kai harin a birnin Dams.10 mai 2012.

Akalla mutane 55 ne aka kashe a yayin da wasu sama da 372 suka jikkata a yau alhamis, sakamakon wasu hare-haren ta’addanci da aka kai da bam a birnin Damas babban birnin kasar Suriya, kamar yadda ministan cikin gidan kasar ya bayyana a wata sanarwa ta tashar talabijin din gwamnatin kasar.Majiyar ta bayyana cewa, hare haren guda 2 da aka kai da sanyin safiyar yau alhamis a birnin na Damas, na kunar bakin wake ne, suka tashi bama baman da suka dana a motoci, wanda aka kiyasta cewa sun kai nauyin kilo gram 1000.Tashar Talabijin din gwamnati kasar ta Suriya ta kara da cewa, bayan abkuwar harin sama da bahuna 15 ne aka makare da sassan jikin yan adam din da harin ya rutsa da su.Manzon kasashen duniya kan sasanta rikicin yakin basasar kasar ta Syriya Kofi Anan, ya tir da Allah waddai da harin da gwamnatin Bashar Al’assad ta dora alhakin kaishi a kan yan tawayen da ke kiyayya da gwamnatinsa.