Iraki

An gano gawwakin wasu mutane 7 dauke da harbin bindiga ga kai a kasar Iraki

AFP PHOTO/FAROOQ KHAN/POOL

Mahukumtan kasar Iraki sun bayyana cewa, a yau Alhamis sun gano gawwakin wasu mutane 7 da aka kashe ta hanyar harbin Bindiga a kai, bayan da aka daure masu hannuwa da idanu, a rairayin saharar yankin tsakkiyar kasar.Wani jami’in tsaro da ya ki ya bayyana sunansa ya shaidawa Kamfanin dillancin Labaran AFP cewa, sun gano gawawwakin mutanen ne a yankin Saddamiyat al-Tharthar, dake arewacin Falluja, dukkaninsu kuma hannuwansu da Idanunsu a daure, tare da raunukan harbin bindiga a kai.Wani jimi’in kiyon lafiya a babbar asibitin Ramadi ya tabbatar da karbar gawawwaki da aka aje a mutuware.Garuruwan Falluja da Ramadi dai, na cikin yankin al-Anbar dake yammacin kasar Iraki ne, yankin da ya taba zama tingar yan tawayen Sunni, a lokacin da kasar Amruka ta mamaye kasar a 2003.