Indonesiya

An fara neman gawarwakin wadanda suka mutu a hadarin jirgin Indonesiya

Tsaunin Salak na Indonesiya, da jirgin saman kasar Rasha ya fadi
Tsaunin Salak na Indonesiya, da jirgin saman kasar Rasha ya fadi Reuters

A kasar Indonesia, a yau juma’a masu aikin ceto, dauke da jikkunan zuba gawarwaki sun fara isa zuwa tsaunin nan da jirgin saman kasar Rasha, dauke da mutane 45 ya fadi. Ma’aikatan na anfani da kayan hawan tsauni, don hawa tsaunin Salak, da ke kudancin birnin Jakarta, kuma an ce suna gab da kaiwa inda gawarwakin fasinjojin jirgin suke.Kwamandan sojojin da ke aikin, kanar Anton Mukti Putranto yace wasu daga cikin ma’aikatan nashi suna hawa tsaunin daga kasa yayin da wasu, da suka je kololuwar shi, suke saukowa, inda za su hadu da juna.