Pakistan-Indiya

Kasar Pakistan ta ce zata koma tuburin tattaunawa da Indiya dangane da tsaunin Siachen

A yau juma’a kasar Pakistan ta bayyana cewa a ranar 11 zuwa 12 ga watan yunin gobe ne, za a koma wata sabuwar tattaunawa tsakaninta da kasar Indiya dangane da tsaunukan Siachen, dake dankare da dussar kankara a yankin Himalaya, da makwabtan kasashen 2 da basa ga maciji da juna ke jayayya akansa yau da shekaru 30 da suka gabata.Kiran kaushe sojojin da ke dankare da dakarun kasar Indiya da Pakistan, dake yiwa juna kallon hadarin kaji ba tare da sun gwabza fada ba a tsaunin na Siachen mai tsawon mita dubu 6000, inda kasashen ke ci gaba da kaurara yawan sojojinsu tun bayan faruwar hadarin da ya yi sanadiyar mutuwar sojoji da fararen hular kasar Pakistan 140 a farkon watan Avrilun da ya gabata.