Falesdinawa-Isra'ila

Falesdinawa sun kawo karshen yajin cin Abinci a gidan yarin Isra’ila

Wata Zanga Zanga da Falesdinawa suka gudanar a Zirin Gaza domin neman sakin 'Yan uwansu da ake tsare dasu a Isra'ila
Wata Zanga Zanga da Falesdinawa suka gudanar a Zirin Gaza domin neman sakin 'Yan uwansu da ake tsare dasu a Isra'ila Reuters/Mohammed

Falesdinawa 1,500 da ke yajin cin abinci a gidan yarin Isra’ila, sun kawo karshen fafutukarsu, bayan kwashe sama da watanni biyu, saboda wata yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Isra’ila da Falasdinu.

Talla

A karkashin yarjejeniyar, Isra’ila ba zata sake tsawaita ci gaba da tsare su, ba tare da yi musu shari’a ba.

Rahotanni sun ce, yarjejeniyar ta biyo fargabar da ake da shi na tashin hankali, muddin wani daga cikin Falesdinawan ya mutu a gidan yari sanadiyar yajin cin abinci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.