Yemen

Mutane 96 sun mutu a wani harin kunar bakin wake a Yemen

'Yan Sanda sun kewaye harabar dandalin da Sojoji ke Fareti a Sanaa babban birnin Yemen
'Yan Sanda sun kewaye harabar dandalin da Sojoji ke Fareti a Sanaa babban birnin Yemen REUTERS/Khaled

Jami’an kiwon lafiya a kasar Yemen sun ce akalla mutane 96 suka mutu sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai a sansanin Soji a birnin Sanaa. Rahotanni sun ce mutane da dama sun ji rauni bayan da Bom ya tashi da wani mutum sanye da kayan Soji a dai dai harabar inda Sojoji ke maci a Sanaa.

Talla

Yanzu haka dai wadanda suka ji rauni an kwashe su zuwa asibitin Taxis. Ana tunanin an kai harin ne domin shugaban kasa Abd Rabbu Mansour Hadi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.