Iran-IAEA

Tawagar masu sa Ido ta IAEA sun kai ziyara Iran game da nukiliya

Yukiya Amano Babban Darektan hukumar Makamashi ta IAEA ta majalisar Dinkin Duniya
Yukiya Amano Babban Darektan hukumar Makamashi ta IAEA ta majalisar Dinkin Duniya DIETER NAGL / AFP

Tawagar masu sa Ido akan makamin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, sun isa kasar Iran, Domin duba Rumbunanta na ajiye makamai. Ziyarar ta masu sa Idon karkashin jagorancin Yukiya Amano tana da manufar shawo rashin fahimtar da ake samu tsakanin kasashen Duniya da Iran game da nukiliya.

Talla

Wannan dai shi ne karon farko da wannan Tawagar a karkashin jagorancin Yukiya Amanos, ke kai irin wannan ziyarar da manufar sake tattaunawa tsakanin Iran da hukumar makamashi ta IAEA.

Manufar wannan ziyarar ita ce sake fito da kwakkwarar dabarar yadda za’a sa kasar ta Farisa ta amsa tambayoyin hukumar IAEI, kan shirin Iran na Nuclear mai saikakiya.

Ziyarar ta Tawagar Amano dai ta zo ne a yayin da ake kokarin fara tattaunawar Iran da manyan kasashen Duniya a birnin Baghdad, a sati mai zuwa.

Hukumar IAEA tace na’urar hango bayannai ta Satelite, ta hango wani abu mai hatsari da rikitarwa a kasar Iran, a yayin da Iran ke musanta aukuwar hakan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.