Iran-Irak

kasashen Iran da Iraki sun yi masayar Gawawwakin dakarunsu a yakin da kasashen 2 suka gwabza a 1980-1988

Kasahen Iran da Iraki a yau talata sun yi masayar gawawwakin sojoji 111 da aka kashe a lokacin yakin da kasashen 2 suka gwabza a 1980 zuwa 1988, kamar yadda kungiyar bayar da agajin jinkai ta Croix-Rouge da kuma ma’aikatar ministan kare hakkin dan adam ta kasar Iraki suka sanar.

Talla

Sanarwar ta bayyana cewa, sauran gawawwakin dakarun kasar Iran 98 da na Iraki 13 da suka kwanta damar a yakin shekaru 8 da kasashen biyu suka gwabza a yau talata ne, aka yi masayarsu a kan hanyar Chalamja kusa da Bassora na kasar Iraki, a karkashin sa idon kungiyar bayar da agajin jinkan ta Croix rouge international.

Masayar gawawwakin ya hadu da wasu shagulgula da suka samu halartar wakili ma’aikatar ministan kare hakkin dan adam ta kasar Iraki a Basora, Mahdi al Tamimi da kuma wani janar din sojan kasar Iran, Mohamed Bagir Zada.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.