India

Mutane 14 sun mutu, 40 sun samu rauni a wata taho mugama da jirage suka yi a India

Wani Jirgin kasa na indiya wanda ya kashe wani Bafaranshe daya gitta a titin jirgin
Wani Jirgin kasa na indiya wanda ya kashe wani Bafaranshe daya gitta a titin jirgin AFP

A kalla mutane 14 ne suka mutu, fiye da 30 suka sami raunuka, lokacin da wani jirgin kasa mai daukar Fasinja ya yi karo da wani jirgin mai daukar kaya a yau Talata a arewacin kasar.

Talla

Wani ma’aikacin tashar jirgin ya shada wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP cewa cikin wadanda suka mutu har da wani karamin yaro, da ke cikin jirgin mai zuwa Bangalore.

Yace lamarin ya faru yau da Asuba, kuma yanzu haka masu aikin ceto sun riga sun kai wajen, don fitar da wadanda hadarin ya rutsa da su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.