Rikicin Syria

Shugaban Syria Bashar al Assad.
Chanzawa ranar: 28/05/2012 - 14:27

A ranar 15 ga watan Maris shekarar 2011 al’ummar Syria suka fara zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad. Amma hankali kasashen Duniya ya rabu biyu game da hanyoyin da za’a bi wajen kawo karshen zubar da jini tsakanin dakarun Gwamnati da ‘Yan Adawa. Majalisar Dinkin duniya tace sama da mutane 10,000 ne suka mutu tun fara zanga-zangar. Irin wannan zanga-zangar ce ta yi awon gaba da gwamnatin Zaine El Abiden ben Ali na Tunisia da Hosni Mubarak na Masar Kanal Gaddafi na Libya.