Yemen-Alka'ida

Ana ci gaba da tabka fada tsakanin dakarun gwamnatin Yemen da na kungiyar Alka'ida

taswirar yankin 'Abyan dake  kudancin kasar  Yamen tare da mashigin ruwar arabiq
taswirar yankin 'Abyan dake kudancin kasar Yamen tare da mashigin ruwar arabiq RFI/Archimède - Camjusan / I. Artus

A kalla yan tawayen kasar Yemen 35 ne suka gamu da ajalinsu, a fada da aka gwabza a cikin daren jiya laraba a yankin kudancin gunduman Abyan, a fafatawan da dakarun kasar ke yi domin sake kwace yankunan da ‘yan tawaye suka kwace.

Talla

Majiyoyi daban daban sun bayyana cewa, dakarun gwamnatin kasar yanzui haka suna ci gaba da dannawa gaba wajen ganin sun kori mayakan kungiyar Al-Qaeda dake ci gaba da mamaye wasu sassan kasar.

Kamfanin Dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa, tun ranar da aka fara a gwabzawar wato ranar 12 ga wannan watan mutane akalla 299 suka gamu da ajalinsu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.