Pakistan

Kotun Pakistan ta yanke hukuncin daurin shekaru 33 ga Likitan da yasa aka kashe Osama

Photo non datée ni localisée du docteur Shakil Afridi.
Photo non datée ni localisée du docteur Shakil Afridi. REUTERS/Geo News via Reuters

Wani likitan kasar Pakistan, da ya taimaka wa jami’an leken asirin Amurka CIA, suka zakulo Osama bin Laden zai shafe shekaru 33 a gidan yari. Kotun ta sami Shakeel Afridi da laifin cin amanar kasa, zai kuma biya tarar dalar Amurka dubu uku da dari Biyar.

Talla

A watan Yulin bara ne Afridi ya shirya wani shirin allurar rigakafin karya, da aka yi amfani da shi wajen daukar kwayoyin hallitar mutanen gidan da ake zargin a nan ne Bin Laden ya ke boya. hakan kuma ake hasashen ya sa aka kai harin a gidan, aka kashe shugaban kungiyar Al-Qaeda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.