Faransa-Afghanistan

Shugaban Faransa ya kai ziyarar ba zata a Afghanistan

Shugaban Faransa François Hollande, a lokacin da yake ganawa da Dakarun Faransa a Afghanistan
Shugaban Faransa François Hollande, a lokacin da yake ganawa da Dakarun Faransa a Afghanistan REUTERS/Joel Saget

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, ya kai wata ziyarar bazata a kasar Afghanistan, inda ya gana da dakarun kasar da shugaban yace zasu fice daga Afghanistan a karshen shekara. Wannan ita ce ziyararsa ta farko a Afganistan a matsayin shugaban Faransa.

Talla

Ana saran Hollande zai gana da shugaba Hameed Karzai, bayan ganawa da dakarun Faransa

Sabon shugaban ya bayyana shirinsa na janye dakarun kasar daga Afghanistan, tun lokacin da yake yakin neman zabe, kuma ko a taron kungiyar NATO makon jiya, bai yi kasa a gwiwa ba, wajen tirjewa kan matsayinsa.

Nan da kwanaki ne ake sa ran fitar da sabon jadawalin tsarin kwanakin da dakarun Faransa zasu fara ficewa daga Afghanistan.

Dakarun Faransa Tamanin da Uku ne suka mutu tun kaddamar da yaki a shekarar 2001 bayan kai harin 9 ga watan Satumba a kasar Amurka.

An fi samu yawan mutuwar Fararen hula ‘Yan kasar Afghanistan fiye da dakarun NATO. Kuma Majalisar Dinkin Duniya tace a bara fararen hula 3,021 suka mutu.

Kuma sanadiyar rikicin Afghanistan yasa daruruwan ‘Yan kasar yin gudun hijara tare da neman mafaka a makwabtan kasashe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.