MDD-Syria

Kofi Annan zai gana da Bashar Assad na Syria

Kofi Annan, Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke jagorantar  sasanta rikicin kasar Syria
Kofi Annan, Tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya wanda ke jagorantar sasanta rikicin kasar Syria Reuters

Ana sa ran Kofi Annan, Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Syria, zai gana da shugaba Bashar al assad, bayan kisan kiyashin da aka samu a Huola, wanda ya janyo suka daga sassan duniya. Bayan isar Annan Syria a jiya, Annan ya gana da Ministan harkokin wajen, Walid Muallem, da kuma shugaban tawagar masu sa ido, Janar Robert Mood inda ya bukaci gaggauta aje makamai.